Mutane 28 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Hatsarin Jirgi a Gabashin Rasha

 

Babu wanda ya tsira bayan da wani jirgi da ke dauke da mutane 28 ya yi hadari a gabashin Rasha a ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha ya Ambato jami’an ceto na cewa.

Jirgin mai suna Antonov 26 na kan hanyarsa daga babban birnin yankin Petropavlovsk-Kamchatsky zuwa Palana, wani kauye a arewacin tsibirin Kamchatka, lokacin da aka daina jin duriyarsa, in ji ma’aikatar bada agajin gaggawa ta Rasha.

Kamfanin dillacin labaran Rasha na Interfax ya ruwaito cewa ana tunanin jirgin ya fada cikin wani dutse ne a lokacin da yake shirin sauka a cikin wani yanayi na rashin kyawun gani.

Hukumar kula da zirga -zirgar jiragen sama ta kasar Rasha ta tabbatar da cewa an gano inda jirgin ya fadi bayan da ma’aikatar agajin gaggawa ta aike da jirgi mai saukar ungulu tare da tura tawagogi a kasa don nemansa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here