Jami’ar Jahar Ondo ta Sanya Dokar Hana Saka Kayan da Basu Kamata ba a Jami’ar

 

Hukumar gudanarwar jami’ar Adekunle Ajasin ta jahar Ondo, ta sanya dokar hana sanya matsatstsun kayan da basu kamata ba a jami’ar.

An yi tanadin dauar matakin dakatarwa a kan duk dalibin da aka samu da saba wannan doka.

Cikin wata sanarwa da aka raba wa daliban jami’ar mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Satumban nan, jami’ar ta nuna damuwa kan yadda ta ce dalibai na yawan yin shigar da bata kamata ba a makaantar.

Sanarwar ta ce bayan zuzzurfan bincike, wannan makaranta ta yanke shawarra cewa daga yanzu za a dakatar da duk wanda aka samu da saba wannan ka’ida tsawon wata guda, farawa daga ranar 25 ga watan Agusta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here