Hatsarin Jirgin Ruwa ya yi Ajalin Mutane Huɗu a Jihar Nasarawa

 

Jirgin ruwa ya ƙara gamuwa da hatsari a jihar Nasarawa ranar Litinin, aƙalla mutane huɗu sun riga mu gidan gaskiya.

Ganau ya bayyana cewa waɗanda suka mutu suna hanyar zuwa taimaka wa ɗan uwansu a aikin gona lokacin da lamarin ya rutsa da su.

Shugaban matasan yankin ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen ɗaukar matakan kaucewa faruwar haka nan gaba.

ihar Nasarawa – Mutanen da basu gaza huɗu ba sun rasa rayuwarsu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Litinin a jihar Nasarawa.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wannan ya sa haɗurran jirgin ruwan da ya faru a jihar a baya-bayan nan ya kai 16 jumulla.

Daga cikin mutum huɗun da suka rasu a sabon haɗarin, biyu ƴan uwan juna ne na jini watau iyayensu ɗaya yayin da sauran biyun sun fito daga ƙauyen Ubbe, ƙaramar hukumar Nassarawa Eggon.

Idan baku manta ba makamancin wannan hatsarin ya rutsa da fasinjojin jirgin ruwa a Kogi Kungra Kamfani da ke yankin Arikiya, ƙaramar hukumar Lafiya.

A wannan hatsarin na baya, mutane 19 ne suka rasa rayukansu yayin da aka samu nasarar ceto mutun Bakwai a raye, kamar yadda Daily post ta ruwaito.

Yadda sabon hatsarin jirgin ya faru

Ganau ya bayyana cewa mutum huɗun da suka mutu a haɗarin jirgin ranar Litinin da ta gabata, sun yi niyyar zuwa yankin ne domin taimaka wa ɗan uwansu.

A cewar shaidan gani da ido, sun taho ne da nufin zuwa yankar shinkafar ɗan uwansu yayin da hatsarin ya rutsa da su lokacin da zasu ketare kogin.

Wani dan uwa ga waɗanda suka rasu sanadin haɗarin kuma shugaban matasan yankin, Kwamared JD Congo, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba (yau).

Ya kuma roki gwamnatin jihar Nasarawa da ta samar da matakan da ya dace domin kaucewa sake afkuwar irin haka a nan gaba.

“Ina kira ga gwamnatin jihar Nasarawa da darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar da su dauki matakan da suka dace don dakile kwararowar ruwa daga dam din Lagdo na ƙasar Kamaru.”

“Bisa haka ina rokon gwamnati da ta kara kaimi wajen samar da jiragen ruwa na zamani, da rigunan ceto, da kuma rundunar ruwa domin tabbatar da tsaron mazauna yankin,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com