Hatsarin Mota ya Rutsa da ɗaliban Jami’ar Najeriya, ya yi Ajalin Mutane 5

 

Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane biyar a jihar Bayelsa ranar Jumu’a 28 ga watan Afrilu, 2023.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin motocin da haɗarin ya rutsa da su ta ɗauko ɗaliban jami’ar Neja Delta ta nufi Yenagoa.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce suna fara bincike kan abinda ya haddasa hatsarin.

Bayelsa – Mutane 5 sun mutu a wani mummunan haɗarin Mota da ya rutsa da su a kan titin Amassoma-Tombia da ke yankin ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa.

Daily Trust ta tattaro cewa haɗarin, wanda ya auku ranar Jumu’a da yamma, ya rutsa da Motar Mazda mai ɗauke da kusan mutum 7 ciki har da ɗaliban jami’ar Neja Delta (NDU).

Motar da ɗaliban ke ciki ta taso ne daga garin Amassoma, kudancin ƙaramar hukumar Ijaw zuwa Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Motar ta yi taho mu gama da wata motar toyota SUV baƙa wacce ta nufi garin Amassoma, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here