Hauhawar Farashin Kayan Masarufi ya ƙaru Zuwa Kashi 25.80 a Najeriya – NBS
Adadin hauhawar farashin kaya a Najeriya ya karu zuwa kashi 25.80 cikin 100 a watan Agusta idan aka kwatanta da na watan Yulin 2023 wanda ya tsaya a kashi 24.08, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana.
Rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ya karu da maki 1.72%.
Read Also:
Ya kara da cewa a duk shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 5.27 cikin dari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Agustan 2022, wanda ya kai kashi 20.52 cikin dari.
Ta ce hauhawar farashin abinci a watan Agustan 2023 ya kai sama da kashi 29 cikin dari, wanda ya kai sama da kashi 6 bisa dari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Agustan 2022 wanda kashi 23.12 cikin dari ne.
NBS ta lura cewa hauhawar farashin kayan abinci a kowace shekara ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin mai da burodi da hatsi da kifi da ganyeyyaki da sauran kayan abinci.