Hukumar Hisbah ta Jahar Kano ta Kama Motoci 2 Dauke da Kwalaben Giya 5,760

 

Hukumar Hisbah ta Jahar Kano ta ce ta samu Nasarar kama Motoci biyu ƙirar J5 maƙare da giya.

Babban kwamandan Hisbah a Kano Dr Harun Ibn-Sina, cikin wani hoton bidiyo da yake bayani ya ce kimanin Kwalbar giya 5,760 jami’an hukumar suka kama kan hanyar Madobi a ranar Laraba.

Hisbah ta sha kamawa da tarwatsa kwalaben giya a jahar Kano

Shugaban Hisbah ya jaddada cewa an haramta shan giya da sayar da ita a faɗin Kano, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙi da duk wata baɗala a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here