Bayan Karbar Mulki a Afghanistan: Saudiyya ta yi Magana Kan Gwamnatin Taliban

 

Saudiyya ta ce tana fatan gwamnatin riƙon ƙwarya a Afghanistan za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kawo ƙarshen tashin hankali da tsattsauran ra’ayi.

Ministan harakokin wajen Saudiyya ne ya bayyana haka a wani taron ministoci kan rikicin Afghanistan.

Yarima Faisal bin Farhan ya kuma jaddada goyon bayan Saudiyya kan abin da ya kira “zaɓin mutanen Afghanistan kan makomar ƙasarsu da kuma tsira daga katsalandan na wasu ƙasashen waje,” kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya rawaito.

Taliban dai ta razana ƙasashen yammacin duniya kan yadda ta naɗa tsoffin mayaƙanta masu tsaurin ra’ayi a manyan muƙamai a sabuwar gwamnatin da ta kafa, cikinsu har da waɗanda Amurka ke nema ruwa a jallo.

Yarima Farhan ya ce Saudiyya mai ƙarfin faɗa a ji a Gabas Ta Tsakiya na da matuƙar muhimmanci ga tasirin taimakawa Afghanistan magance ƙalubalen da ke gabanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here