HIV: Wadanda Cutar ta fi Kamawa #UNFPA
A ranar Talata, UNFPA ta ce kashi 50 bisa 100 na masu HIV karuwai ne da ‘yan luwadi.
A cewarta, dole ne duk mai kanjamau ya kiyaye kansa daga COVID-19 don za ta iya ajalinsa.
Darektan UNFPA, Dr Natalia Kanem ce ta shaida hakan a Abuja, a ranar kanjamau ta duniya.
A ranar Talata, UNFPA tace kashi 50 bisa 100 cikin wadanda basu dade da samun kanjamau ba, karuwai ne da ‘yan luwadi.
Sai dai ta yi takaicin sanar da cewa kaso kadan ne daga kudaden da aka ware don shawo kan HIV za a sadaukar garesu, jaridar Vanguard ta tabbatar.
Read Also:
UNFPA ta bayyana hakan a wata takarda wacce darektan ta, Dr Natalia Kanem ta gabatar a Abuja ta zagayowar ranar kanjamau ta duniya ta shekarar 2020, wacce tayi wa take da, “Kawo karshen cutar HIV/AIDS: Janyo masu cutar a jiki, da kwantar musu da hankali.”
UN ta bayyana yadda masu HIV za su fi saurin kamuwa da cutar COVID-19 kuma ta illata su.
Kanem ta ce mafi yawan wadanda suke samun cutar HIV a fadin duniya, karuwai ne da kuma maza ‘yan luwadi.Suna samun cutar ne sakamakon yin jima’i da mutane daban-daban.
“Alamu sun nuna cewa babban hatsarin da masu HIV za su fuskanta shine idan suka kamu da COVID-19 don hakan zai iya sanadiyyar mutuwarsu cikin kankanin lokaci.”
A cewarta, matsawar ana son kawo karshen HIV, wajibi ne a dinga janyo masu cutar a jiki.