Muna Bukatar Lokaci Don Horar da Makiyaya Kan Yadda za a Daina Yawon Kiwo a Fili – MACBAN ga Gwamnatin Legas
Kungiyar Miyetti Allah a jahar Legas ta roki gwamnatin jahar da ta daga musu kafa kan dokar hana kiwo sakaka.
Wannan na zuwa ne yayin da jahar Legas ke kokarin sanya dokar hana kiwo sakaka a dokokin jahar.
Kungiyar Miyetti Allah ta ce, za ta koma ta koyar da mambobinta yadda ake kiwo a wuri daya cikin gaggawa.
Legas – Sashin kudu maso yammaci na kungiyar makiyaya shanu ta Miyetti Allah (MACBAN) ta ce tana bukatar lokaci don horar da membobinta kan yadda za a daina yawon kiwo a fili, TheCable ta rawaito.
Maikudi Usman, sakataren shiyyar MACBAN na kudu maso yamma, ya yi rokon ne a ranar Laraba 8 ga watan satumba a wurin taron jin ra’ayin jama’a na dokar hana kiwo a jahar Legas.
Read Also:
Ya ce membobin kungiyar suna bukatar lokaci don a karantar da su kan “yadda za su yi kiwo a wuri daya kuma ba za su taka kasar kowa ba”.
A cewar Usman:
“Makiyayanmu ba su saba da kiwon shanu wuri daya ba. Suna tafiya ne daga nan zuwa wani wuri. Idan muka ce za mu ajiye shanu wuri daya, mai shanun ba zai sami kudin ciyar da dabbobin a wuri daya ba.
“Sun riga sun dogara da tafiya daga wannan wuri zuwa wani. Domin a lokacin damina, muna da inda muke sauka, kuma muna da inda muke sauka a rani.
“Muna rokon gwamnatin jahar Legas da ta ba mu lokaci mu je mu fada wa mutanenmu kuma mu horar da su yadda za su yi kiwo a wuri daya kuma kada su fada zuwa kasar kowa. “Amma kiwo a wuri daya, a yanzu, mutanen mu ba su da ikon yin hakan. Abin da ba ku saba da shi ba, dole ne a koyar da ku. Kuma a hankali, kowa zai fahimta. ”
A ranar Litinin, dokar hana kiwo sakaka ta wuce karatu na biyu a majalisar dokokin jahar Legas.
Idan an zartar da kudirin, Legas za ta shiga cikin wasu jahohi a yankin kudancin kasar da suka sanya dokar hana kiwo sakaka a cikin doka.