Hukumar Gidajen Gyara Halin Najeriya ta Sake Hotuna da Sunayen Fursunonin da Suka Gudu.

 

Hukumar gidajen gyara halin Najeriya ta nuna alamun ta shirya damke fursunonin da suka gudu da gidan garin Owerri.

Hukumar na kira ga jama’a su taimaka wajen tona asirin duk wanda suka gani cikinsu.

Har yanzu mutum guda aka kama cikin wadanda suka tsere daga gidan yari Sakamakon ballewa daga gidan yarin garin Owerri, jahar Imo da wasi fursunoni sukayi, hukumar gidajen gyara halin Najeriya ta sake hotuna da sunayen fursunonin da suka gudu.

Hukumar NCS a ranar Juma’a, 9 ga Afrilu, ta shafinta na Tuwita, ya saki hotunan wasu da sunayen fursunonin.

Legit.ng ta kawo muku yadda wasu yan bindiga suka balla gidan yarin Owerri ranar 5 ga Afrilu kuma suka saki Fursunoni 1,884.

Amma kawo ranar Alhamis, 78 cikin fursunonin sun koma da kansu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here