Hujjar da Yasa Buhari Bazai Murabus Ba – Lai Mohammed
Daga karshe gwamnatin tarayya ta yi martani a kan kira ga murabus din shugaba Buhari.
Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya yi bayani kan dalilin da yasa Shugaban kasar ba zai yi murabus ba.
Mohammed ya dasa ayar tambaya kan kudirin masu kira ga Buhari ya sauka daga mulki.
Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa duk da kiraye-kiraye da ake yi na yayi murabus.
Da yake magana a wajen wani ganawa da kungiyar mamallakan jaridun Najeriya (NPAN) a Lagas a ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba, Mohammed ya ce kira da ake na Shugaban kasar yayi murabus siyasa ce.
Read Also:
A cewar jaridar Punch, ya bayyana bukatar Shugaban kasa yayi murabus kafin kammala wa’adin mulkinsa saboda kisan wasu manoma a jihar Borno a matsayin rashin tunani.
Mohammed yace:
“A tsaka da lamarin kashe-kashe, ana ta kira a wasu bangarori kan Shugaban kasar yayi murabus.
“Don haka, bari na fadi cewa wannan kira shiri ne na buga kazamar siyasa da lamarin tsaro, kuma hakan rashin tunani ne.
An zabi Shugaban kasar a 2015 na tsawon shekaru hudu sannan aka sake zabarsa a 2019 don ya sake wasu shekaru hudun.”
Ya jaddada cewa babu yawan kira da za a yi masa na yayi murabus da zai hana Shugaban kasar cike wa’adinsa.
Ministan ya ce kokarin janye hankali da kazamar siyasa ce ke sa ake neman Shugaban kasar ya sauka daga mulki a duk lokacin da aka samu akasi a yaki da ta’addanci.