Hukumar Lafiya ta Duniya za ta yi Taron Gaggawa Kan Cutar Marburg

 

Hukumar lafiya ta duniya ta ce za ta yi taron gaggawa a kan barkewar cutar Marburg a Jamhuriyar Equatorial Guinea da ke yankin tsakiyar Afirka.

Alkaluman hukuma sun nuna cewa zuwa yanzu cutar ta hallaka mutum tara, kuma akwai wasu mutum 16 da ake fargabar sun kamu da zazzabin a lardin Kie Ntem na gabashin kasar, inda a baya ba a samu bullar cutar ba.

Bincike ya nuna an samu mutuwar ne sakamakon wata jana’iza da mutanen hudu ‘yan gida daya suka halarta ta wanda cutar ta yi sanadin mutuwarsa.

An yi amanna cutar na yaduwa ne zuwa mutane daga jimage da ke cin ‘ya’yan itace, da kuma irin yadda Ebola ke yaduwa tsakanin mutane ta hanyar ruwa ko yawu ko majina ko jinin jikinsu.

Ya zuwa yanzu cutar ta Marburg mai haddasa tsananin zazzabin ba ta da magani ko riga-kafi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here