Hukumar Kula da Sufuri ta Jiragen Kasa a Najeriya ta Kawo Babban Cigaba

Hukumar kula da sufuri ta jiragen kasa a Nigeria (NRC) ta dauki babban mataki domin kawo karshen matsalar magudin sayar da tikiti.

Matafiya na yawan kokawa akan yadda wasu ma’aikatan NRC ke tafka cuwa-cuwa ta hanyar boye tikiti tare da kara masa kudi.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya tabbatar da cewa an bullo da tsarin da zai bawa matafiya damar siyen tikiti ta yanar gizo.

Chibuike Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya tabbatar da cewa hukumar kula da sufuri ta jiragen kasa a Nigeria (NRC) ta bullo da sabon tsarin siyen tikiti kai tsaye ta shafinta na yanar gizo.

Amaechi ya fitar da wani takaitaccen sako a sahfinsa na tuwita (@ChibuikeAmaechi) domin tabbatar da cewa da gaske ne NRC ta fara gwajin tsarin siyen tikitin jirgin kasa daga shafinta na yanar gizo.

“Eh, da gaske ne an bullo da tsarin siyen tikitin jirgi daga shafin hukumar NRC, an fara gwada tsarin a cikin wannan satin kafin kaddamar da shi gaba daya a mako mai zuwa. Ku ziyarci shafin NRC a https://nrc.tps.ng domin siyen tikiti ko ganewa idonku,” kamar yadda Amaechi ya wallafa.

Ana ganin bullo da wannan sabon tsari zai magance korafin cuwa-cuwar tikitin jirgi da wasu ma’aikatan NRC ke yi a tashohin jiragen kasa, musamman a Abuja da Kaduna.

Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, 2021, ta rattaba hannu akan bayar da kwagilar gina titin jirgin kasa na zamani daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar da kuma daga Kano zuwa Dutse, babbn birnin jahar Jigawa.

Kamfanin da aka bawa kwangilar aikin, Mota-Engil Group, ya dauki alkawarin ginawa Nigeria Jami’a kyauta kafin kammala kwangilar da aka bashi.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya sanar da hakan yayin da ya wallfa hotunansa yayin saka hannu akan kwangilar a shafinsa na dandalin sada zumunta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here