Hukun Kirsimeti: Adadin Kwanakin da Gwamnatin Tarayya ta Bada

Gwamnatin tarayya ta bada hutun bukukuwar Krsimeti, Ranar bada kyaututuka (Boxing Day), da kuma sabon shekara.

Ranakun hutun sune Juma’a 25 da Litinin 28 ga watan Disambar 2020, sai kuma ranar Juma’a 1 ga watan Janairun 2021.

Gwamnatin ta janyo hankulan ‘yan Najeriya kan darrusan da bukukuwan suka kunsa tare da shawartarsu su kiyaye dokokin yadda korona.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 25 ga wata da Litinin 28 ga watan Disamban 2020 da Juma’a 1 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranakun hutu don bikin Kirsimeti, Boxing Day da kuma Sabon shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwar da sakataren dindindin na ma’aikatar Dakta Shuaibu Belgore ya rattaba hannu a kai a ranar Laraba.

A yayin da ya ke taya kiristan Najeriya da na kasashen waje murnar bikin Kirsimetin da Sabon shekara, Aregbesola ya bukaci kiristoci su yi koyi da koyarwar Annabi Isa da suka hada da imani da kauna.

“Ya zama dole muyi koyi da rayuwar kankan da kai, hidima, tausayi, hakuri, zaman lafiya da tsoron Allah da Annabi Isah (AS) ya siffantu da su, wannan shine hanya mafi dacewa da za mu yi murnar zagoyowar ranar haihuwarsa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa zaman lafiya da tsaro abubuwa ne da ke da muhimmanci da za su bawa gwamnati daman farfado da tattalin arziki, janyo hankulan masu saka hannun jari da samar da ayyuka da miliyoyin matasan Najeriya cikin shekaru 10 masu zuwa.

Aregbesola ya kuma janyo hankulan ‘yan Najeriya su cigaba da bin dokokin hukumomin lafiya da gwamnati na kare yaduwa annobar corona da ta dawo a karo na biyu musamman a lokaci irin na bukukuwa.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here