Hukuncin da Amurka ta Ɗauka Kan Matar da ta Zubar da Ciki
A lokacin da aka kama matashiyar Ba’amurkiyar nan yar Oklahoma da ke Amurka da laifin kisan kai bayan ta zubar da ciki, mutane sun rika ta da jijiyar wuya.
Brittney Poolaw mai shekaru 21 ta rasa ɗanta watanni hudu da samun ciki a watan Janairun 2020.
Amma kuma a watan Oktoba aka yanke mata hukunci dauri na shekara hudu bisa kamata da laifin kisan kai.
Ta samu kanta daga cikin bakin cikin yin bari, zuwa shan dauri da zargin kisan kai, wanda hakan ya tada kura sosai a kafafen yada labarai.
A lokacin da ta isa asibiti neman magani, Poolaw ta fadi cewa ta rika amfani da magunguna masu hadari ga masu ciki.
Daga baya binciken likitoci da BBC ta samu ya nuna cewa ta yi amfani da methamphetamine, kamar yadda aka gano a hanta da ƙwaƙwalwar ɗan tayinta.
Lauyoyin Poolaw sun ce za su daukaka kara, duk da har yanzu mai shigar da kara ya ƙi ya ce uffan kan batun.
To amma labarin Poolaw somin tabi ne, a cewar Dana Sussman, ta kungiyar National Advocates of Pregnant Women (NAPW), mai fafutuka kan kare ‘yancin mata masu ciki.
“Shari’ar Britney ta taba mu sosai, abun ya wuce yadda mutane ke tunani,” in ji ta.
Kungiyar na taimakawa wurin bibiyar daukaka shari’ar Poolaw, kuma tana ci gaba da bibiyar irin wadannan shari’o’i da suka shafi mata masu ciki.
Daga 1973 zuwa 2020, NAPW ta shedi kararraki 1,600, kuma 1,200 sun faru ne a cikin shekaru 15 da suka wuce.
Duk da cewa laifukan sun shafi mata masu ciki da suka haihu a gida, mafi yawa sun fi karkata kan shan kwayoyi masu hadari kuma da dama matan da ba ‘yan asalin Amurka ba ne abin yafi shafa.
Tasirin magunguna da masu ciki ke sha ga jarirai
Magungunan da masu ciki ke sha na da tasiri kan abin da ke cikinsu, wanda ka iya haifar da bari ko kuma haihuwar bakwaini.
Kazalika ƙwayoyi kamar cocaine sun haifar da matsala ga jariran da mata masu shan kwayar ke haihuwa, kamar yadda wani bincike da aka gudanar a shekarun 1980 ya nuna.
Ana ayyana amfani da magunguna masu hadari da masu ciki ke amfani da su a matsayin cin zarafin yara, kuma jihohi 23 a Amurka na amfani da wannan doka.
Ana kirkirar irin wadannan dokoki da nufin hukunta masu taimakawa wurin cutar da yara tun suna ciki.
Irin wadannan matakan horarwa sun kara fitowa fili a 2004, lokacin da aka zartar da hukunci biyo bayan mutuwar Laci Peterson, wadda ake zargi cewa mijinta ya kashe ta.
Inda matsalar take ita ce ana samun rudani kan yadda ake amfani da dokokin a wurare daban-daban.
Jihohi a Amurka sun saka wa’adin da ciki zai shafe da ya haramta a zubar dashi, to amma likitoci da dama sun tafi ne akan makonni 20 zuwa 24.
Read Also:
Cikin Poolaw na cikin mako na 16 ne zuwa 17 a lokacin da ta yi bari, wanda shi ne farko-farkon wa’adin da aka shata na kama mace da laifi a Amurka.
Da a ce Poolaw zubar da ciki ne ta yi ba bari ba, kwata-kwata ba za a kama ta ba saboda zubar da ciki ba laifi ba ne a Oklahoma.
To amma yanzu haka ana jiran kotun koli ta zartar da hukunci kan badakalar haramta zubar da ciki a Texas, da kuma tsaurara matakai a wasu jihohi.
Sai dai masu fafutuka na fargabar cewa ana kokarin bullo da wani tsari na hana mata ‘yancinsu.
A kasashen da aka haramta zubar da ciki, ana kama mata da daure su da laifin kisan kai saboda sun yi bari.
Ana zargin su da yin bari dagangan, ta hanyar shan kwayoyin da ke lalata cikin.
An kama matar da ta zubar da ciki a El Salvador kuma a gidan yari ta mutu
A El Salvado ma na daya daga cikin kasashen da suka tsaurara sosai kan zubar da ciki, inda yanzu haka kasar ke shari’a da wata mata a kotun kasa da kasa da ke kare hakkin bil’adama ta Inter-American Court of Human Rights.
An yanke wa Manuela shekaru 30 a gidan yari da laifin kisan kai, a lokacin da aka kamata a asibiti neman magani bayan da ta yi ɓari.
Daga baya Manuela ta mutu a gidan yari a shekarar 2010.
Lauyoyinta sun ce dokar El Salvador ta cewa likitoci su kai rahoton matan da suke zargin sun zubar da ciki ko kuma su likitocin su sha dauri, ya saba wa dokar kare hakkin bil’adama ta duniya.
Sai dai masana kamar su Emma Milne ta jami’ar Durham da ke Burtaniya, na ganin cewa mata masu ciki ba sa samun taimakon da ya kamata a ce hukumomi sun basu a lokacin da suke fadi tashi da cikin.
“Maganar gaskiya gwamnatoci sun gaza wurin bai wa mata taimakon da suke bukata yayin da suke da ciki, akan haka ba dai dai bane a rika kallon matsalar jaririn da ke cikinsu ba su kuma a yi ko oho da ta su, in ji ta.
Wani bincike da aka kaddamar a 2012 ya nuna cewa kashi shida na masu ciki a Amurka a lokacin sun bayyana cewa suna shan kwayoyi masu illa ga cikinsu, yayin da kashi 8.5 suka bayyana cewa suna shan giya, kashi 16 kuma suka ce suna shan taba sigari.
A nata bangaren kungiyar likitoci ta Amurka ta nuna adawa da bayyana shan kwayoyi masu illa ga ciki a matsayin cin zarafin kananan yara.
Kungiyar ta US medical association ta kuma ce magani ya kamata a nema wa irin wadannan mata a maimakon kai su gidan yari.
Akwai ma lauyoyin da ke ganin cewa bai dace a bai wa jaririn da bai gama zama mutum ba dama iri daya da cikakkar mace ba.
“Babu mai tababa cewa jariran za su zama mutane cikakku, amma abun tambaya shine shin doka ta ayyana su a matsayin mutane?”, a cewar Glenn Cohen, masanin harkar lafiya a makarantar aikin lauya ta Harvard Law School a Amurka.
Ya kara da cewa “a ƙaddara cewa doka ta ba su damar, shin ya dace ace damarsu ta shiga gaban ta matan da ke dauke da su?”.
A kan haka masu fafutuka ke ganin cewa kawai an siyasar da batun ne, saboda haka dole a fahimci cewa mace mai ciki na da cikakken ‘yanci wanda a yanzu ake kokarin ƙwace mata.