Anas Darazo
Ba mamaki kai ma idan wata jarrabawa ta same ka haka zasuyi maka irin yanda sukai ma IG Wala. Idan kana so ka gane yanda mutane zasu mu’amalance ka bayan mutuwar ka ko tashin ka a wurin zama ko fadawa cikin matsala to ka duba yanda sukai bayan dayan hakan ta faru da wanin ku. Ita jarrabawa babu wanda yafi karfin ta, duk irin kuskuren da kaga IG yayi shi kana iya aikata sama da shi, babu irin jarrabawar da rayuwa bata zuwa da shi, ai shiga masifa ba na marasa imani bane kawai balle kace kai mai imani ne ka tsira.
Read Also:
Hausawa dai cewa sukai ba’a dariya a motar gawa, sun auna sun gano kowa na iya shiga a kowane lokaci, amma fa duk wanda ya dauke ta abun dariyar ce ku barshi ya kyakyata ya dara. Yawanci mu fa muna zuri’a da dangi, idan mu bama kwamranci ko aktibisinci irin haka bamu da masaniyar cewa wani cikin dangin mu yanayi ko zaiyi nan gaba? Idan ya fada irin haka hala damu za’ai musu (Yan uwan nwmu) gwalo, watakil kuma haushi zamu ji muce ba’ai mana jaje ba ba’a kyauta mana ba. Abunda ya kamata mu sani fa shine ba iya hanyar da IG Wala yabi bane ake zuwa kurkuku, a’a a hanyar cin abincin ka (kasuwar ka ko office din ka) kana iya haduwa da tsautsayi ka tafi kurkuku, baka lura bane wasu a hanyar addinin Allah suka tafi gidan maza ba?
Humanity! Humanity!! Ina humanity din namu? Ina tausayi da jinkai na musulunci da Dan Adamtaka? Ina Yan uwantaka ta addini? Ina sabo da shakuwa irin ta zumuncin soshiyal media? Ashe duk bula ce? Wani zaice IG ya girbi abunda ya shuka ne, eh amma ka sani ba IG nake karewa ba, mamaki da tsoron mune ya kama ni lokacin da naga muna raha da zolaya saboda bala’in da wani ya shiga, tausayin mune ya kama ni saboda naga zahirin irin abunda wasun mu zasuyi idan wanin wanin mu ya shiga matsala, rashin tausayi da rashin hangen nesan mu na gani.
Muji tsoron Allah, idan ba zamu taimaki mutane a matsalar su ba kada mu musu dariya, idan ya zama dole sai mun musu kuma mu sani zamu iya shiga don haka mu shiryawa karban tamu dariyar ketar.
Anas Darazo
18-04-2018
The post Hukuncin da aka yankewa IG Wala ba abin dariya bane appeared first on Daily Nigerian Hausa.