Hukuncin da Zamu Dauka kan Kyari – Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta bayyana irin hukuncin da za ta iya dauka kan Abba Kyari.
A cewarta, za ta iya korarsa kai tsaye ko rage masa matsayi kamar yadda dokar aikin ta tanada.
A halin yanzu ana ci gaba da bincike kan zargin da ake wa Abba Kyari na karbar cin hanci a hannun Hushpuppi.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta bayyana cewa kora kai tsaye na daya daga cikin hukuncin da ka iya hawa kan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP), Abba Kyari, idan aka same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da Kyari kwanan nan bayan da Amurka ta gabatar da zarginsa da hannu a zambar dala miliyan 1.1 da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushipuppi ya aikata.
A bangaren Kyari, ya karyata dukkan wasu tuhume-tuhumen da ake akansa.
Read Also:
Sai dai, Austin Braimoh, mai magana da yawun PSC ya yi magana game da matakan ladabtarwa da Kyari zai iya fuskanta idan aka kama shi da laifi dumu-dumi.
Braimoh ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa hukuncin da ake yiwa jami’an ‘yan sandan da suka aikata irin tuhumar da ake wa Kyari sun hada da gargadi, tsawatarwa, tsawatarwa mai tsanani, rage matsayi, da kora kai tsaye.
Ya ce abin bakin ciki ne cewa masu yaki da aikata miyagun laifuka a wasu lokutan kan tsunduma cikin barna a karshen cikin rashin kulawa.
Amma mai magana da yawun PSC ya nuna cewa ba daidai bane a yanke cewa DCP Kyari ya aikata laifi ba tunda har yanzu ba a gurfanar da shi a karkashin dokokin Najeriya ba.
Braimoh ya bayyana cewa tuhumar da ake wa Kyari a kotun Amurka na bukatar a bi dokokin Najeriya da farko don tabbatar da ko dan sandan ya aikata laifi kamar yadda ake zargi.
Ya lura cewa zai zama abin takaici idan aka samu dan sandan da ake yaba aikinsa a kasar.