Mene ne Hukuncin Saɓa wa Dokar Faɗin Albarkacin Baki?

A kwanakin nan, batun kama mutane saboda iƙirarin faɗin albarkacin bakinsu ya sake janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya, musamman bayan da aka zargi gwamnatin Neja da kama wani matashi da ake zargin ya yi ihun ”babu ruwa babu wuta”.

Lamarin ya faru ne a lokacin wata ziyara da gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ya kai garin Suleja na jihar.

Ba wannan ne karo na farko da irin wannan lamari ke faruwa ba a Najeriya.

A lokuta da dama, an kama ƴan Najeriya saboda bayyana ra’ayoyinsu kan shugabanni, gwamnati ko yadda ake tafiyar da al’amuran ƙasa.

An kuma samu rahotannin kama wasu ‘yan Najeriya bayan sun yi kalamai masu zafi ko suka soki wasu shugabannin ƙasashen waje, ciki har da firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

Wannan ya ƙara faɗaɗa muhawara kan yadda ‘yancin faɗin albarkacin baki ke aiki da kuma ci gaba da tayar da tambayoyi kamar haka:

Mene ne ma’anar ƴancin faɗin albarkacin baki?

Wananna al’amari ya sake haifar da tambayoyi game da mene ne ainihin faɗin albarkacin baki, da kuma lokacin da yake zama laifi?

Kan haka ne BBC ta tuntuɓi, Barista Sadiq Abba Usman, wani lauya mai zaman kansa a ƙasar, wanda kuma ya ce ƴancin faɗin albarkacin baki ƴanci ne wanda ƙundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar wa kowanne mutum da ke rayuwa a ƙasar.

”Kuma akwai dokokin Majalisar Dinkin Duniya da kuma na Tarayyar Afrika wanda suka tabbatar duk wani ɗan’adam wannan ƴancin faɗin albarkacin bakinsa”, in ji shi.

Lauyan ya ce ƙarƙashin waɗannan dokoki, kowanne mutum yana da damar tofa albarkacin bakinsa ya faɗi ra’ayinsa a kan ƙasarsa ko gwamnatin ƙasarsa ko a kan kansa ko kan yadda ake tafiyar da ƙasa ya bayyana farin cikinsa ko baƙin cikinsa ko ya yi fashin baƙi a kan yadda ake gudanar da gwamnati.

Kalaman da suka saɓa wa yancin albarkacin baki

Barista Sadiq ya ce dokar Najeriya ta tanadi dokoki da matakai domin tabbatar da cewa an yi amfani da ‘yancin faɗin albarkacin baki cikin tsari.

Ya bayyana cewa wannan ƴanci ba ya nufin a yi magana ba tare da la’akari da illar da za ta iya biyo baya ba.

”Duk wanda ya yi amfani da ƴancin faɗin albarkacin baki wajen yaɗa ƙarya, ƙage ko ƙazafi, ko kuma ya yi magana wanda yake akwai tsangwama a cikinta akan wani mutum ko gwamnati, ko ya faɗi abin da ba daidai ba wanda zai iya kawo tashin hankali a cikin al’umma, to ya wuce iyaka, kuma doka na da tanadin hukunci a kansa,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa wannan na nufin akwai dokoki da aka kafa domin kare mutunci da zaman lafiya a cikin al’umma.

Sai dai ya jaddada cewa sukar gwamnati ko shugabanni ba laifi ba ne.

A cewarsa maganganu kamar ”ba ruwa”, ”ba wuta” ”ba ma yi”, ga shuwagabanni ko ga gwamnati, a tsarin doka, ba abu ne wanda yake laifi ba, hasali ma abu ne wanda ɗan ƙasa yake da kariya daga ƙundin tsarin mulki na ya bayyana ra’ayinsa game da irin waɗannan abubuwa.

Barista Sadiq ya ƙara da cewa ainihin tsarin dimokraɗiyya shi ne bai wa jama’a damar faɗar abin da ke ransu, ko na goyon baya ko na suka.

“Idan babu wannan ƴanci, to abin da ake kira dimokraɗiyya ba ya wanzuwa, abin da ke akwai shi ne mulkin kama karya,” in ji shi.

Dokoin ƴancin faɗin albarkacin baki

Barister Sadiq ya lissafo wasu daga cikin dokoin ƴancin faɗin albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada:

Kada mutum ya yi maganar da za ta haifar da tashin hankali ko rikici a al’umma

Kada mutum ya yi zagi ko ɓata sunan wani

Kada mutum ya yi kalaman da zai tayar da zaune-tsaye ko ƙarfafa aikata laifi

Kada mutum ya saɓa dokokin tsaron ƙasa

Kada mutum ya yaɗa ƙarya ko ƙage ko ƙazafi ko tsangwama a cikin maganganunsa.

Mene ne hukuncin saɓa wa dokar faɗin albarkacin baki?

Barista Sadiq Abba ya ce idan aka samu mutum da laifin saɓa wa dokokin ƴancin faɗin albarkacin baki, akwai hukuncin da aka tanadar masa da suka haɗa da

Kamawa da gurfanarwa a kotu

Tara idan laifin bai yi tsanani ba

Ɗaurin kurkuku, musamman idan maganar ta haddasa rikici ko barazana ga tsaro

A wasu lokuta, ana iya tuhumar mutum da laifukan da suka shafi ɓata suna ko kuma haddasa tarzoma

Ta yaya mutum zai gane abin da yake faɗa ya saba wa doka?

Barista Sadiq ya bayyana cewa mutum na iya gane lokacin da abin da yake faɗi zai saɓa wa doka ta hanyar nazarin gaskiyar abin da yake furtawa da kuma tasirinsa ga wasu.

Ya ce, “idan maganar da mutum yake yi ba ta da tushe ko hujja, akwai yiwuwar ta saɓa wa doka.”

A cewarsa, duk wata magana da ta ƙunshi ƙarya da ƙage ko sharri ko ƙazafi ga wani mutum ko gwamnati na iya jefa mai furta ta cikin matsala ta shari’a.

“Duk lokacin da ka san abin da kake faɗa ba gaskiya ba ne, ko kuma ba za ka iya tabbatar da shi ba, to ka san cewa kana hanyar saɓa wa doka” in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan mutum zai faɗi albarkacin bakinsa, to ya tabbatar yana da hujja da gaskiya.

Wato kafin mutum ya faɗi wani abu, ya tambayi kansa ko yana da abin da zai tabbatar da maganarsa idan aka kai shi gaban kotu.

“Dole ne mutum ya kasance yana da hujjoji da zai iya kare kansa da su, idan aka nemi bayani,” a cewarsa.

Ya ce, “faɗin ra’ayi ko sukar gwamnati ba laifi ba ne, amma abin da doka ta hana shi ne karya, ƙazafi da kalaman da za su iya tayar da fitina a cikin al’umma.”

Barista Sadiq ya shawarci mutane su riƙa yin hattara da kalamansu, musamman a wannan zamani na kafafen sada zumunta inda magana ke saurin yaɗuwa.

“Kafin ka yi magana, ka tabbatar da gaskiyarta, ka kuma yi la’akari da illar da za ta iya haifarwa,” in ji shi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here