Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Matashin da ya Saci Baro
An damke wani matashi a jihar Bauchi kan laifin satar baron da ake amfani wajen aikin dako.
Kotun Shari’a dake jihar ta yanke masa hukuncin daurin watanni bakwai a gidan kurkuku.
Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da akwai kotunan Shari’ar Musulunci.
Read Also:
A jihar Bauchi, an gurfanar da wani matashi mai suna AbdulJalal Sadiq ka laifin satar Baron dako.
Leadership ta rawaito cewa an gurfanar da shi ne gaban kotun Shari’ar ta II dake jihar.
Bayan amsa laifinsa, Alkalin mai shari’a, Mukhtar, ya yankewa Abduljalal Sadiq hukuncin daurin watanni bakwai a gidan kaso .
Alkalin ya bashi zabin biyan tara N7,000 da bulala 12 gaban kotu.