Hukuncin da Kotun Kasar Marocco ta Yanke wa ‘Yan Ci-rani 33
Wata kotu a Morocco ta yanke wa wasu ‘yan ci-rani 33 hukuncin daurin wata 11 saboda shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Read Also:
A watan da ya gabata ne dai wani kwale-kwale ya kife a tekun kasar makare da ‘yan ci-rani, a kokarinsu na shiga Turai, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu.
Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Airka da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha yin Allah-wadai saboda yadda jami’an tsaron Morocco da na Sifaniya ke amfani da karfin da ya wuce kima kan ‘yan ci-ranin.