Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Sadiya Haruna

 

Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta damki wata ‘yar wasan kwaikwayo na Kannywood, Sadiya Haruna wacce ta shahara a kafafen sada zumunta.

Hukumar ta kama ta ne bisa laifin yada hotuna da kalaman batsa a shafukanta na sada zumuntar zamani tun ranar Juma’a har ranar Litinin.

Bayan ta amsa laifinta ne aka yanke mata hukumcin komawa Islamiyya ta yi karatun addini har na tsawon watanni shida.

Kano – Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta damki jarumar Kannywood, kuma sun garkame ta sakamakon yada hotunan batsa da take yi a shafukanta na kafafen sada zumunta.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, tun ranar Juma’a jami’an hukumar suka kama ta tunda dama ita mazauniyar Kabuga ce dake Jahar Kano.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa, sun cigaba da rike ta har ranar Litinin kafin suka mika ta zuwa kotun musulunci don a yanke mata hukunci a Sharada.

Sadiya ta amsa laifi daya ciki tarin laifukan da ake zarginta da aikata wa wanda hakan ya ci karo da sashi na 355 na kundin Penal code na 2000.

Alkali Ali Jibril Danzaki ya yanke mata hukunci tare da umartar ta da komawa Islamiyya don ta yi karatu na tsawon watanni shida.

Sannan dole ne kullum jami’an Hisbah za su dinga rakata zuwa Islamiyyar domin tabbatar da ta je Islamiyyar sannan shugaban makarantar zai kiyaye da zuwanta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here