Hukuncin da Kotu ta Yankewa ‘Dan Ta’addan Boko Haram

 

Bayan kimanin shekaru biyar, kotu ta kammala Shari’a kan dan ta’addan Boko Haram a jahar Ekiti.

An kama dan ta’addan da laifin kashe jami’in da sanda da kuma mallakan muggan makamai.

Alkalin yace hujjoji sun bayyana karara cewa shi ya aikata wannan laifi kuma hukunci ya hau kansa.

Oye Ekiti – Wata kotu dake zamanta a jahar Ekiti ta yankewa wani dan ta’addan Boko Haram mai suna Abdulsalam Adinoyi, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkali Lekan Ogunmoye, ya yanke wannan hukunci ranar Laraba a babban kotun jahar dake Ado Ekiti, rahoton Premium Times.

An tuhumi dan ta’addan wanda shi ya bayyana cewa shi dan Boko Haram ne da laifuka biyar; fashi da makami, kisan kai, ta’addanci, da amfani da makamai.

A hukuncin Alkali Lekan Ogunmoye, yace hujjojin lauyoyin gwamnati suka gabatar ya nuna cewa lallai wanda ake zargin ya aikata laifukan da ake zarginshi da su.

Lauyoyin sun bayyana cewa Adinoyi tsakanin ranar 22 ga Disamba 2016 da 20 ga Maris 2017, ya yi amfani da bindiga wajen kawai wani jami’in dan sanda Gana Jiya da abokan aikinsa a Oye Ekiti hari.

Ya kashe Sajen Jiya a wajen yayinda sauran yan sanda sukayi mumunan jigata. Adinoyi ya bayyanawa kotu cewa lallai shi dan Boko Haram ne.

A hukuncinsa, Alkalin yace:

“Mun kama wanda ake zargin da laifi, kuma saboda haka an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Allah ya jikansa.”

Daga cikin abubuwan da aka samu hannunsa akwai kasukan atisayen yan Boko Haram, layukan waya biyar, jakar harsasai, dss.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here