Makarantar Lauyoyi ta Najeriya za ta Hukunta Dalibin da ya Kafa Baki a Gorar Ruwa

 

Makarantar Horas Da Lauyoyi Ta Najeriya da ke Legas ta tura wa wani dalibinta wasikar neman ba’asin dalilin da yasa ya kafa baki ya sha ruwa daga gora a wurin cin abinci duk da akwai kofi a tebur a gabansa.

NLS

Wasikar da mahukuntar makarantar lauyoyin suka tura da ya bazu a intanet ya ce abin da dalibin ya aikata ya saba wa saba doka ta 6 (29) na kudin tarbiyya na daliban makarantun lauyoyi na Najeriya kan tarbiyar cin abinci da halayya.

Makarantar ta bukaci dalibin ya amsa wasikar cikin awanni 24 da samunta ya bayyana dalilin da yasa ba za a hukunta shi ba saboda saba dokar.

Jihar Legas – Makarantar Horas da Lauyoyi Ta Najeriya da ke Jihar Legas, a halin yanzu tana bincike kan wani dalibi da ya sha ruwa daga gora a wurin liyar cin abinci.

Binciken zai iya sanadin mahukunta makarantar su dakatar da dalibin, SaharaReporters ta ruwaito.

Wani takardar neman jin ba’asi da mahukunta makarantar suka aike wa daliban, da ya bazu a intanet, ya ce dalibin ya saba doka ta 6 (29) na kudin tarbiyya na daliban makarantun lauyoyi na Najeriya kan tarbiyar cin abinci da halayya.

“An kai wa Direktan kuma shugaban sashin karatu a ranar 16 ga watan Yunin 2022 cewa yayin liyafar cin abinci na dalibai masu karattun lauyoyi a dakin cin abinci, an gano ka kafa bakinka a robar ruwa a yayin da kofin gilashi na kan teburinka,” a cewar wasikar da wani Fagbemi Charles-Titilayo ya rattaba wa hannu a madadin Direkta kuma Shugaban Sashin Karatu.

“Don haka, ana bukatar ka yi bayanin dalilin da yasa ba za a hukunta ka ba saboda saba wa doka ta 6 (29) ) na kudin tarbiyya na daliban makarantun lauyoyi na Najeriya kan tarbiyar cin abinci da halayya.

“Ka tura dalilanka, idan akwai zuwa ga Direkta kuma Shugaban Sashin Karatu cikin awa 24 da samun wannan wasikar.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here