Yadda Hutun Korona ya yi wa Wani Matashi Rana

Wani matashin dan Najeriya ya gaji da zaman gida sai ya yanke shawaran amfani da lokacin hutu ya shuka doya.

Erhahon ya zabi bayan gidansa domin gwada yin noman lokacin dokar kullen annobar Korona .

Watanni bayan haka, matashin yayi farin cikin girban amfanin gona mai yawa.

Osasere Erhahon, matashi dan jihar Edo, yana matukar farin ciki bayan amfanin da ya samu sakamakon noman doyan da yayi a harabar gidansa.

Erhahon ya yanke shawaran shuka doya a gidansa bayan gajiya da zaman gida lokacin dokar kullen cutar Korona; kawai gwadawa yayi a cewarsa.

A labarin da ya wallafa a Facebook, matashin yayi bayanin yadda doyan yayi girma ba tare da ya sa taki ba ko magani.

“Na girbi wannan doyan a bayan gida na mako jiya a Benin. Na yanke shawaran shuka su lokacin dokar kulle ne saboda gajiya da zama, kuma yanzu na samu alheri sosai, ” Matashin yace.

“Babu taki, babu magani; kawai haka nayi da shuka. Allah na da girma! Najeriya na da kasa mai albarka.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here