Hukumar ICPC ta Kama N170m, Dala $220,965, Mota G-Wagon Daga Hannun ‘Dan kwangilar Soja

 

A babban birnin tarayya Abuja, jami’an hukumar ICPC sun yi babban kamun da ake zargin kayan rashawa ne.

An ruwaito cewa, hukumar ta kama wasu kayayyaki ciki har da motoci da agogi masu matukar tsada ainun.

A cewar hukumar ta ICPC an kama kayan ne a wani samame da jami’an hukumar suka kai kan wani gini.

Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kwato tsabar kudi Naira miliyan 170, dala $220,965, mota G-Wagon da sauran kayayyaki daga hannun wani dan kwangilar soja a Abuja.

Azuka Ogugua, kakakin hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ogugua ya ce bisa ga bayanan sirri, hukumar ta kai samame a wani gida da ke Wuse 2, Abuja, inda aka gano kayayyakin masu tsada.

A cewar sanarwar:

“An jawo hankalin hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) kan wasu rahotannin da ba su da inganci kuma gurbatattu a kafafen yada labarai game da kama wasu kudade biliyoyin nairori, daloli, agogon Rolex da aka jibge a gini a Abuja.

“Hukumar tana so ta bayyana cewa jami’an ICPC sun kai samame kan wani gini a Wuse 2 na babban birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni, 2022 tsakanin karfe 5:00 na yamma zuwa 12:00 na safe bisa zargin karkatar da kudade.

“Bayanan da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa kadarorin mallakar mai kamfanin K Salam Construction Company ne, dan kwangilar soja. “Hukumar ta kwato kudi da wasu kayayyaki daga cikin kadarorin kamar haka, N175,706,500; $220,965; G-Wagon; mota bugun 2022 na BMW da Mercedes Benz; wayoyin hannu na musamman; agogon hannu masu tsada, gami da Rolex uku, da wasu takaddun kadarorin.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here