ICRC ta Bayyana ƙasashen da Suka fi Samun Mutanen da ke ɓata a Duniya

 

Ƙungiyar agaji ta kasa da kasa ICRC ta ce sama da mutu dubu 44 yanzu haka sun ɓata a sassan Afirka – sama da kashi 45 cikin 100 na wannan adadi yara ne.

ICRC ta ce kashi 82 cikin 100 na mutanen da ta dau rajistar ɓatawarsu sun fito ne daga ƙasahe bakwai da ke fama da rikicin ƴan bindiga.

A wata sanawar da ta fitar kan ranar tunawa da mutanen da suka bata a duniya a wannan Litinin din, ICRC ta ce sama da rabin wannan adadi na mutane da suka ɓata ƴan Najeriya ne.

Sauran ƙasashen da aka samu ɓatarwa mutanen sun hada da Ethiopia da Sudan ta Kudu da Somalia da Libya da DR Congo da kuma Kamaru.

Hukumar ta ce nahiyar Afirka na ganin karuwar mutanen da ke ɓatawa a shekarun baya-bayanan saboda rashin zaman lafiya da wasu rigingimun.

Sannan yanayin da ake na annobar korona na dakile kokarin binciko su domin sake sadasu da iyalansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here