Komawa Makaranta: Gwamnatin Jahar Kano ta Kara wa Dalibai Mako Guda

Gwamnatin Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da ɗage ranar komawar ɗalibai makaranta da mako guda.

Kwamishinan Ilimi na jahar, Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, ya ce an tsawaita komawa makaratu da mako guda ne saboda a samu damar daidaita zangon karatun jahar saboda matsaloli da tsaikon da aka rinka fuskanta a lokacin annobar corona.

Sanawar da ya fitar ta umarci ɗaliban da ke makarantun kwana su koma a ranar 12 ga watan Satumba 2021 maimakon 5 ga wata, sannan ƴan je-ka-ka-dawo za su koma ranar Litinin 13 ga watan Satumba 2021 maimakon 6 ga wata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here