Fa’ida 7 da za a Samu Idan Majalisa Ta Amince da Kudirin Sanata Shehu Buba Kan ATBU

Daga Bashir Umar Kirfi
10 Oktoba 2025

A wani mataki mai tarihi da ke da nufin canza tsarin ilimi a yankin Bauchi ta Kudu da ma Jihar Bauchi baki ɗaya, Mai Girma Sen. Shehu Buba umar, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, ya gabatar da kudiri a gaban Majalisar Dattawa domin gyaran dokar kafa Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU).

Manufar kudirin ita ce sauya ATBU daga jami’ar fasaha zuwa jami’a ta baidaya (conventional university) — wani salo da zai buɗe sabbin ƙofofi na ilimi, bincike, da damar ci gaba ga matasa da al’umma baki ɗaya. Kudirin ya tsallake karatu na farko a zauren Majalisar Dattawa, alamar cewa ya samu kyakkyawan karɓuwa daga ‘yan majalisa.

Me Kudirin Ke Nufi?

A cewar Sanata Shehu Buba, gyaran dokar kafa ATBU yana da manufofi masu zurfi da suka shafi faɗaɗa damar ilimi, ƙarfafa tattalin arziki, da samar da ayyukan yi. Kudirin yana da nufin fitar da ATBU daga takurawar karatun fasaha, domin ta koma jami’a da ke koyar da fannoni daban-daban kamar kimiyya, zamantakewa, shari’a, kasuwanci, da al’adu.

Fa’idodi Bakwai Masu Mahimmanci

1. Faɗaɗa Damar Samun Ilimi
Da zarar kudirin ya tabbata, ɗalibai za su sami damar karatu a fannoni daban-daban, ba na fasaha kaɗai ba. Wannan zai taimaka wa dubban matasa da ke neman gurbin jami’a amma ba su da sha’awar karatun fasaha.

2. Samar da Ayyukan Yi
Sauya tsarin jami’ar zai buƙaci ƙirƙirar sabbin kwalejoji, sassa, da ofisoshi, wanda zai haifar da sabbin guraben aiki ga malamai, ma’aikata, da masu aikin kwararru a fannoni daban-daban.

3. Farfaɗo da Tattalin Arzikin Yankin
Faɗaɗa jami’ar zai jawo sabbin kasuwanci, gidajen haya, motocin haya, da otel — lamarin da zai ƙara haɓaka tattalin arzikin Bauchi ta Kudu da Jihar Bauchi baki ɗaya.

4. Ƙarfafa Bincike da Ci gaban Ilimi
Jami’a ta bai daya tana da ikon gudanar da bincike a fannoni da yawa, wanda zai taimaka wajen samar da sabbin dabaru da mafita ga matsalolin da ke fuskantar al’umma.

5. Cika Burin Mutanen Bauchi ta Kudu
Al’ummar Bauchi ta Kudu tun da dadewa suna fatan samun jami’a da ke koyar da fannoni masu faɗi. Kudirin Sanata Buba ya zama amsar wannan buri, alamar jajircewarsa wajen ci gaban yankin.

6. Ƙara Damar Ilimi Ga Mata da Marasa Ƙarfi
Sabbin shirye-shiryen karatu da za a kafa za su buɗe ƙofofi ga mata da matasan da ba su da hali, domin su samu ilimi cikin fannoni da suka dace da su, tare da rage bambanci a damar samun karatu.

7. Haɗin Gwuiwa da Sauran Jami’o’i
Sauya ATBU zuwa jami’a ta baidaya zai jawo sabbin haɗin gwuiwa da jami’o’i a cikin gida da ƙasashen waje, domin musayar ilimi, bincike, da cigaban ƙwarewa.

Sauyi Mai Ma’ana Ga Bauchi da Nijeriya

Wannan kudiri, a cewar Sanata Shehu Buba, ba kawai gyaran doka ba ne — sabuwar hanya ce ta gina makomar ilimi a Bauchi da Najeriya gaba ɗaya.
Ya ce manufarsa ita ce tabbatar da cewa duk wani ɗan Bauchi, musamman matasa, suna da damar samun ingantaccen ilimi wanda zai basu damar zama masu dogaro da kansu.

“Idan muka haɗa kai wajen tabbatar da wannan kudiri, Bauchi za ta zama cibiyar ilimi da ci gaba a Arewa maso Gabas,” in ji wani mai sharhi daga cikin masu goyon bayan shirin.

Ba shakka, kudirin Sanata Shehu Buba Umar ya kasance hangen nesa mai zurfi wanda zai iya zama tushe na sabon salo na ci gaban ilimi a Najeriya.
Idan aka amince da shi, zai baiwa Bauchi damar zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi, bincike da ci gaba a Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here