Kabilar Igbo ta fi Samun Kwanciyar Hankalin Rayuwa da Kasuwanci a Arewacin Najeriya – Ohanaeze Ndigbo

 

Kungiyar kare hakkin yan kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta siffanta Arewacin Najeriya a matsayin wurin da yan kabilarsa suka fi samun kwanciyar hankalin rayuwa da kasuwanci.

Shugaban kungiyar na shiyar jahohin Arewa 19, Augustine Amaechi, a ranar Juma’a a Abuja ya bayyana cewa Arewa ta baiwa Igbo masauki fiye da yadda ake tsammani.

Amaechi ya ce akan samu sabani wasu lokuta saboda a rayuwa dole a samu hakan.

Babu inda Igbo suka fi kwanciyar hankali kamar Arewa, Ohanaeze Ndigbo. UGC A kan maganar ballewar da Igbo ke yunkuri yi daga Najeriya, ya ce rashin ayyukan yi ya sabbaba hakan.

Ya kara da cewa tun da Igbo sun shahara da kasuwanci, suna bukatan Arewa domin tara arziki.

“Magabatanmu na cewa duk da cewa matasanmu sun fusata, muna bukatar garambawul a kasar nan ba ballewa ba saboda ba zaka iya sayar da kayarka a kauyenka ba,” Yace.

Shi kuma shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na kasa, George Obiozor, ya ce al’ummar Igbo ba su yaki da kowa. “Abinda muke so kawai shine daidaito da sauran jama’a. Lokaci ya yi da zamu fadawa shugabanni gaskiya,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here