Babu Wanda ya Bawa Igboho Damar Magana a Madadin Dukkan Yarabawa – Kunle Olajide
Dattawan yarbawa sun ce nesanta kansu da yunkurin fitar da yarbawa daga Nigeria da Sunday Igboho ke neman yi.
Kunle Olajide, Sakataren Kungiyar Dattawan Yarbawa ta YCE ne ya bada wannan sanarwara inda ya ce babu wanda ya bawa Igboho damar magana a madadin dukkan yarabawa.
Olajide ya ce tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka Yarbawa ke zaune da sauran kabilu kuma sun bada gagarumin gudunmawa wurin gina kasar Kunle Olajide, babban sakataren kungiyar Yoruba Council of Elders (YCE) ya ce
Sunday Adeyemo, shugaban matasan yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ba ya wakiltan Yarbawa a yunkurinsa na kafa kasar yarbawa.
Igboho a baya bayan nan ya ce Yarbawa sun fice daga Nigeria, inda ya yi kira ga Yarbawa da ke arewa su dawo gida, The Cable ruwaito.
Read Also:
Da ya ke hira da The Cable a ranar Laraba, Olajide ya ce Nigeria za ta fi karfi idan ta cigaba da zama a matsayinta na kasa guda daya.
a ce Yarbawa sun bada gudunmawa sosai wurin gina Nigeria da hadin kanta don haka babu hikima ta ce za ta fice a kasar a yanzu.
Olajide ya ce: “Wannan ra’ayinsa ne (Igboho) amma halin da muke ciki yanzu hakan ba zai haifar mana alheri ba, kuma dai Yarbawa sun zuba hannun jari mai dimbin yawa wurin hadin kan kasa da gina kasa.
Kabilar ba za ta fice daga kasar ba tare da cikakken shiri ba. “Ban da masaniya kan cewa Yarbawa sun shaida wa wani cewa suna son ficewa daga Nigeria.
Don haka wannan ba shawara bace da yarbawa suka yi. “Duk wanda ya san tarihin Nigeria ya san mun shafe shekaru fiye da 100 tare, tun kafin zuwan turawan Birtaniya akwai Yarbawa da sauran kabilu a sassan Nigeria.
“Wannan ba abinda wani zai iya furtawa bane kawai don kansa. Banbancin kabilu da yawan al’umma shine karfin mu a kasar nan. Rabuwar kai da rarraba kasar ba zai zama alheri gare mu ba.”