‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Uku a Jahar Kaduna

 

‘Yan bindiga sun sake kai hari kananan hukumomin Igabi da Jema’a a jahar Kaduna.

Maharan sun halaka mutane uku a Kauyen Ungwan Lalle sun kuma kashe guda a Golgofa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ya bada sanarwar Wasu yan bindiga sun kai hari a kananan hukumomin Igabi da Jema’a a Jahar Kaduna, inda suka kashe mutane hudu suka raunata wasu da dama, The Punch ta rwuaito.

A cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mr Samuel Aruwam, cikin sanarwar da ya fitar ya ce an kashe mutane uku a kauyen Ungwan Lalle da ke karamar hukumar Igabi.

Ya ce an kai harin ne a safiyar ranar Litinin. Ya ce sunayen wadanda aka kashe sun da da Dayyab Yarima, Dalhatu Ashiru da Suleiman Salamatu.

Kwamishinan ya kara da cewa dakarun sojoji na Operation Safe Haven sun bada rahoton cewa yan bindiga sun kai hari Niima Clinic da ke kauyen Golgofa a karamar hukumar Jema’a a ranar Litinin kuma sun kashe ma’ikaci a asibitin.

Ya ce gwamnan jahar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun labarin ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Ya kuma yi wa wadanda suka samu rauni fatar samun sauki cikin gaggawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here