Bayan Satar Dalibai: IGP ya Kai wa Gwamnan Katsina Ziyara
Babban sifeton rundunar ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya ziyarci jihar Katsina bayan sace dalibai da sakinsu.
A ranar 11 ga watan Disamba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina.
An saki daliban a ranar 16 ga watan Disamba kamar yadda gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya tabbatar.
Babban sifeton rundunar ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya ziyarci hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Katsina domin ganawa da jami’ansa, kamar yadda Channels ta rawaito.
Read Also:
IGP Adamu ya ci alwashin cewa ba za’a kara sace daliban makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara ba a nan gaba.
Bayan ziyararsa, shugaban ‘yan sandan ya gana da kwamandoji, shugabannin bangarori, DPOs, da kwamandojin atisayen Puff Adder domin tattauna yadda za’a kawo karshen aiyukan ta’addnci a Katsina.
Ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta lashi takobin cewa ba za’a kara satar daliban makarantar sakandiren kimiyya ta Kankara ba.
IGP Adamu na wadannan kalamai ne biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, a ranar 11 ga watan Disamba, tare da yin awon gaba da dumbin dalibai.
Daga baya, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da cewa an kubutar da daliban a ranar 16 ga watan Disamba.