IGP ya Gurfanar da Wani Tsohon Gwamna a Gaban Kotu
IGP Mohammed Adamu ya yi karar wani tsohon mataimakin gwamnan Imo, Ikedioha Ohakim a gaban wata babbar kotun FCT.
An gurfanar da Ohakim a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, kan zargin yada labaran karya.
Sai dai kuma ya ki amsa tuhumar da ake masa, an ba tsohon gwamnan beli na naira miliyan 10 A ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedioha Ohakim, a gaban wata babbar kotu a birnin tarayya kan zargin bayar da bayanan karya.
Read Also:
Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ne ya gurfanar da Ohakim a kan wasu tuhume-tuhume uku a gaban kotun da ke Abuja.
Sai dai kuma, mai alkalin da ke jagorantar shari’a, Justis Samira Bature, ta bayar da belin tsohon gwamnan kan naira miliyan 10 bayan ya ki amsa laifinsa, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
An bayar da belin nasa ne a matsayin amsa ga ikirarin lauyan Ohakim, K.C.O Njemanze, wanda ya yi ikirarin cewa tuhume-tuhumen da ake yiwa wanda yake karewa na iya samun beli, matsayar da lauyan mai kara, Stanley Nwodo ya yi adawa da shi.