Gadar Sama: Ilimi da Walwalar Jama’a ce ya Dace ta Zama a Sahun Gaba – Rabi’u Kwankwaso ga Gwamna Ganduje
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jahar Kano, ya zargi shugaba Buhari da rashin gane hoton gadar sama da Ganduje ya kai masa.
Tsohon gwamnan jahar Kano yace alhakin gwamnatin tarayya ne na yin gadar da zata hada garin Kano da na Wudil.
Read Also:
Sanata Kwankwaso ya caccaki Gwamna Ganduje ta yadda bai je wa Buhari da bukatar gadar ba amma zai karbo bashi don yin ta Tsohon gwamnan jahar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin fahimtar hoton da Gwamna Abdullahi Ganduje na jahar Kano ya gabatar masa a fadar shugaban kasan dake Abuja.
Tun a farkon makon nan, Buhari ya karba bakuncin Ganduje wanda ya nuna masa hoton gadar Muhammadu Buhari da za a yi a jahar Kano.
A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso yayi mamakin dalilin da zai sa a karba bashin N20 biliyan a kan aikin nan, wanda yace aikin gwamnatin tarayya ne.
Ya zargi Ganduje da baiwa abubuwan da basu dace ba fifiko inda yace ilimi da walwalar jama’a ce ya dace ta zama a sahun gaba.
“A maimakon Ganduje yaje ya gana da Buhari ya sanar dashi cewa yayi gadar, saboda alhakin gwamnatin tarayya ne yin gadar sama da zata hada garin Kano da Wudil, gwamnan ya tashi ya kai masa hoton da ba a zana da kyau ba, wanda shugaba Buhari bai gane ba.”