Gaskiya Ban ga Illar Abinda Nake yi ba Tsawon Lokaci Har Sai da Jami’an Tsaro su ka Kama ni – Kasungurmin ‘Dan Bindiga

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Katsina ta kama wani kasurgumin dan bindiga, Surajo Mamman wanda aka fi sani da Kutaku.

Kataku ya dade a harkar halaka jama’a da kuma garkuwa da su kamar yadda da bakin sa ya bayyana ranar Laraba.

A cewarsa, be san yawan jama’an da ya halaka ba kuma bai taba sanin babu kyau harkar da yake yi ba.

Katsina – Rundunar ‘yan sandan jahar Katsina ta kama wani jagoran ‘yan bindiga wanda da kan shi ya bayyana yadda ya halaka kuma ya yi garkuwa da mutane da dama kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

Dan bindigan, Surajo Mamman wanda aka fi sani da ‘Kutaku’ mai shekaru 50 da haihuwa ya bayyana cewa shi ne na biyu daga Sani Muhidinge, dan bindigan da gwamnati take nema ido rufe.

Mahinde ya boye ne a dajin Rugu dake tsakanin jahar Katsina da jahar Zamfara.

Jami’an tsaro sun tafi da shi har hedkwatar ‘yan sanda a ranar Laraba a gaban manema labarai.

A cewar sa bai san yawan rayukan da ya halaka ba Kutaku ya amsa laifin sa inda ya ce:

“Na dade ina harkokin garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka. Ba zan iya tuna yawan mutanen da nayi garkuwa da su ko kuma na halaka ba saboda su na da yawa sosai.

“Gaskiya ban ga illar abinda nake yi ba tsawon lokaci har sai da jami’an tsaro su ka kama ni. Amma yanzu ido na ya bude.”

Kamar yadda Sahara Reporters ta rawaito, ya kara da bayyana yadda yake da hannu dumu-dumu a garkuwa da mutane da satar shanaye a kauyakun Dan Musa, Safana, Dutsinma da karamar hukumar Batsari dake jahar Katsina.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here