Mun San Inda ‘Yan Uwan Ahmed Adamu Mu’azu Suke – Kwamishinan ‘Yan Sanda
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi ya bayyana cewa ‘yan sanda sun san inda ‘yan uwan tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Mu’azu suke.
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya kai ziyarar jaje ga iyalan Ahmed Muazu da al’ummar karamar hukumar Tafawa Balewa.
CP Sanda Umar Mamman ya ce ‘yan fashin da suka yi garkuwa da iyalan Adamu Muazu suna neman naira miliyan 600 kafin su sake su.
Jihar Bauchi – Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi CP Umar Mamman Sanda ya bayyana cewa ‘yan sanda sun san inda ‘yan uwan tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Mu’azu suke, inda ya kara da cewa ‘yan fashin na neman naira miliyan 600 kafin su sake su. Rahoton Daily Trust
Read Also:
CP Sanda ya bayyana haka ne jiya a kauyen Boto lokacin da ya raka gwamna Bala Mohammed Abdulkadir domin jajantawa iyalan tsohon gwamnan da al’ummar karamar hukumar Tafawa Balewa kan lamarin.
Ya ce:
“Mun san inda wadanda aka sace suke kuma muna yin iya kokarin mu don kubutar da su cikin koshin lafiya.
Gwamna Mohammed a nasa bangaren ya ce :
“yanzu ‘yan bindigar sun taba gwamnati tunda suka taba iyalan daya daga cikin tsohon gwamnonin mu. Zamu yi iya kokarin mu wajen ceto su.
“Wadannan ’yan iska sun ci mutuncin mu, kuma ba za mu kyallesu ba.
A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan tsohon Gwamnan Bauchi, inda suka kashe kanensa Mua’zu Danladi mai shekaru 25, sannan suka yi garkuwa da ‘yan uwansu uku, Hajiya Asma’u Alhaji Adamu, kanwar tsohon gwamnan, Malama Halima. Abdullahi, da Nura daya.