Sojojin Najeriya Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda a Yankin Jihar Neja
Gwamnan jihar Neja ya bayyana yabonsa ga jaruman sojojin da suka fatattaki ‘yan ta’adda a wani yankin jiharsa.
Rahoto ya ce, an hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da jikkata wasu a lokacin da suka farmaki sansanin sojoji a Neja.
Jihar Neja na da yankunan da ke fama da barnar ‘yan ta’adda a shekarun nan, an sha dasa sojojin domin shawo kan lamarin.
Minna, jihar Neja – Abubakar Bello, gwamnan jihar Neja, ya ce dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari da wasu ‘yan tada kayar baya suka kai a wani sansanin soji da ke yankin Sarkin Pawa a jihar.
A cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN), hakan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Noel-Berje, ta fitar a ranar Litinin 18 ga watan Yulin 2022.
TheCable rahoto cewa, Bello ya ce maharan sun yi yunkurin kai hari ne a kwaryar garin da kuma kan sansanin sojojin da misalin karfe 2:23 na safiyar ranar Litinin.
Read Also:
Ya ce sojojin da suka amsa kiran gaggawa sun isa garin Sarkin Pawa cikin mintuna 30, kuma an kashe da yawa daga cikin maharan a wani artabu da suka yi.
Yadda lamarin ya faru A cewarsa:
“Harin da aka kawo zai yi muni idan da ba don gaggawar mayar da martani daga gwarazan sojojin da ke Sarkin-Pawa da kuma tawagar da suka yi gaggawar amsa kira ba.
“Ba a samu asarar rai a bangaren sojoji ba yayin da aka ce an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
“Amsa kiran gaggawar da sojojin da ke Munya suka yi da kuma martanin da rundunar ta yi game da kiran da suka yi daga Minna abin a yaba ne.”
Ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na shawo kan lamarin duk da yanayin da suke ciki na yakar makiya a jihar, Daily Sun ta ruwaito.
Ya kara da cewa:
“Gwamnatin jihar Neja ta yaba da kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaki da rashin tsaro a jihar.”
Ya kuma tabbatar wa da mazauna jihar cewa jihar na hada hannu da gwamnatin tarayya domin ganin an kawar da ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare a yankunan manoma da lalata hanyoyin more rayuwa.