Wata fitacciyar ‘yar siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Hajiya Naja’atu Mohammed ta ce babu gaskiya cikin yaki da gwamnatinsu ke yi da cin hanci da rashawa.
Hajiya Naja’atu Muhammad na cikin wadanda suka rika tallata Muhammadu Buhari a matsayin mafi cancanta da zama shugaban kasa a zaben 2015.
‘yar siyasar ta yi wannan jawabi ne dangane da jerin bidiyon da aka wallafa da ke zargin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudaden da aka ce cin hanci ne daga hannun ‘yan kwangila.
Ta kalubalanci gwamnatin tasu a kan rashin gudanar da bincike kan lamarin, duk da ikirarin da jami’anta ke yi da cewa suna yaki da rashawa.
“Idan zargi ne, me ya sa ba a yi bincike ba? Ai, idan ba a yi zargi ba, ba za a yi bincike ba. Idan ba a yi bincike ba, ai ba za a gano gaskiya ba.”
Ta ce a iyakar saninta, kotu ba ta isa ta hana ‘yan sanda bincike ba.
Read Also:
A cewarta da ma ta san majalisar dokokin jihar Kano ba da gaske take yi ba wajen gudanar da binciken lamarin, don kuwa ‘yan sanda ne suke da hakkin yin bincike.
Tun da farko, majalisar dokokin Kano ta kafa kwamiti don gudanar da bincike kan lamarin sai dai wata kotu ta dakatar da ita inda ta ce ba ta da hurumi.
Sai dai Hajiya Naja’atu ba daidai ba ne hukumar EFCC ta juya baya a kan wannan batu, don kuwa ita da ‘yan sanda suna da ikon su yi bincike don tabbatarwa ko wanke zargin da ake yi.
Ta ce ita ba ta yarda ba satar da dukiyar jama’a ba, ko daga wacce jam’iyya yake.
“Maciji duk maciji ne, kowanne ne daga PDP yake ko daga APC, zai yi sara ne ya cutar da mutane. Azzalumi, azzalumi ne. Kunama ce idan za ta harbe ki, ko wacce irin tuta ta dauka, sunanta kunama. Kisa za ta yi!
Ni a ce an bar wani saboda kawai yana APC, ni wannan ban yarda da shi ba. Saboda an zalunci, zalunci ne.”
The post Indai da gaske ake yaki da cin hanci da rashawa a binciki Ganduje – Najatu Mohammed appeared first on Daily Nigerian Hausa.