An Bai wa Shugaban ƙasar Indiya Wa’adin Sanya Hannu Kan Dokokin Jihohin ƙasar

 

Kotun ƙolin Indiya ta bai wa shugaban ƙasar wa’adin wata uku da ya amince da sabbin dokoki da jihohin ƙasar suka amince da su.

Akwai tarin ɗaruruwan dokoki da waɗanda jihohin ƙasar da dama suka amince da su – da suka ɗauki shekaru a ofishin shugaban ƙasar – suna jiran sanyawar hannun shugaban.

Akwai rahotonnin da ke cewa an riƙe dokokin ne saboda bambancin siyasa tsakanin gwamnatocin jihohin da kuma gwamnatin tarayya.

Masana fannin shari’a na cewa hukuncin kotun ƙolin tabbatar da damar jihohin ne na yin dokoki.

Jihar Tamil Nadu ce dai ta shigar da ƙara gaban kotun ƙolin, inda bayanai ke nuna cewa tana da muhimman dokoki 10 da ke jihar sanyawar hannun shugaban ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here