Bayelsa: INEC ta Cire Jam’iyyar APC Daba Zaben Maye Gurbin Kujeran Sanata

Hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta cire jam’iyyar All Progressives Congress APC da dan takarata Peremobowei Ebebi, daga musharaka a zaben kujerar dan majalisan dattawa mai wakiltan mazabar Bayelsa ta yamma.

Shugaban sashen yada labarai na INEC dake Bayelsa, Wifred Ifogah, ya sanar da hakan ranar Alhamis yayinda yake gabatar da jawabi madadin kwamishanan INEC na jihar.

An shirya yin zaben Bayelsa ta tsakiya da Bayelsa ta yamma ne ranar 31 ga Oktoba amma aka dage zuwa 5 ga Disamba sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

Ifogah yace hukumar ta yanke shawaran cire APC ne saboda hukuncin babban kotun tarayya dake Yenagoa. Ya ce kotun ta haramtawa hukumar sanya APC da dan takararta a takardar zabe.

Saboda haka, Ifogah ya ce jam’iyyu 12 kadai za suyi musharaka a zaben.

Babbar kotun tarayya dake Yenagoa karkashin jagorancin Alkali Jane Inyang, a ranar 3 ga Nuwamba ta dakatad da Peremoboei Ebebi na jam’iyyar APC daga takarar zaben kujerar Sanatan Bayelsa ta kudu kan zargin amfani da takardun bogi.

Kotun ta yi watsi da zaben fidda gwanin da ya ci.

Peremoboei Ebebi ya kasance tsohon mataimakin gwamnan jihar.

Amma kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC ta yi alla-wadai da wannan hukunci na INEC inda tace wannan zalunci ne.

Diraktan yakin neman zaben, Offini Williams, ya ce hukumar ya tsunduma cikin siyasa saboda babban kotu ba ita bace kotun koli ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here