Hukumar INEC ta Cire Sunan Doguwa Daga Jerin Sunayen ‘Yan Majalisar Wakilai
Hukumar zaɓen Najeriya ta cire sunan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa daga cikin jerin sunayen zaɓaɓɓeun ‘yan majalisar wakilan ƙasar da suka yi nasara a zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.
Hukumar zaɓen ƙasar ce dai tun da farko ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Read Also:
Jami’in tattara sakamakon zaɓen Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya bayyana cewa Doguwa na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 39,732, inda abokin takararsa na jam’iyyar NNPP Yushau Salisu Abdullahi ya samu ƙuri’a 34,798.
To sai dai a jerin sunayen zaɓaɓɓun ‘yan majalisun da hukumar zaɓen ta fitar a shafinta na Twitter, babu sunan Alhassan Ado Doguwa a cikin jerin ‘yan majalisun.
INEC ɗin ta ce an tilasta wa jami’in tattara sakamakon zaɓen wajen bayyana sakamakon da ya bai wa Doguwa nasara a zaɓen da aka gudanar.