Maganar INEC kan Yawan ‘Yan Takara a 2023

Hukumar zaɓe INEC ta ce ko kaɗan ba ta damu da yawan yan takarar dake neman shugaban ƙasa ba a zaɓen 2023.

A cewar hukumar mai zaman kanta, jam’iyyun siyasa 18 ne halastattu, dan haka su ne kaɗai zasu gabatar mata da yan takarar su.

INEC ta ce yawan yan takara ya shafi jam’iyyun siyasa domin su ke da alhakin gudanar da zaɓen fidda gwani.

Abuja- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, (INEC), ta ce ƙaruwar mutanen dake nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 be dame ta ba.

INEC ta ce jam’iyyun siyasa 18 ne kacal halastattun da za su gabatar mata da yan takarar su a tseren kujera mai daraja ta ɗaya a Najeriya, kuma kowace jam’iyya ɗan takara ɗaya zata tsayar.

A wata hira da jaridar Leadeship a Abuja ranar Lahadi, Sakataren watsa labarai na shugaban INEC ta ƙasa, Rotimi Oyekanmi, ya ce:

“Jam’iyyun siyasa 18 ne kaɗai zasu gudanar da zaɓen fidda gwani, dan haka su kaɗai hukumar zata sanya wa ido.”

Aikin jam’iyya ne shirya zaben fidda gwani – INEC

Oyekanmi ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa ne ke da nauyin shiryawa da gudanar da zaben fitar da ɗan takara bisa tanade-tanaden dokokin zaɓe da tsarin jadawalin INEC.

“Saboda haka, idan masu neman kujerar shugaban ƙasa suna da yawa, ya wajaba kan jam’iyyun su na siyasa su bi matakan tsayar da mutum ɗaya, dan haka abun yana kan su ne.”

“Mun yi shirin sa ido a zaɓen fidda gwani 18 ko abin da bai kai haka ba, ya danganta da jam’iyyun da suka sanar da mu za su gudanar da zaben cikin lokacin da aka ƙayyade.”

Ya ƙara da bayanin cewa alhakin hukumar INEC ne da sa io domin tabbatar da jam’iyyu sun bi matakan ta hanyar da doka ta tanada.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here