Hukumar INEC ta Sha Alwashin Magance Matsalar Sayen ƙuri’a a Zaɓen Bana
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sha alwashin magance matsalar sayen ƙuri’a a zaɓen ƙasar da ke tafe, ta hanyar haɗa hannu da hukummomin da ke yaƙi da cin hanci da almundahar kuɗade na ƙasar ICPC da EFCC.
Hukumar ta bayyana sayar da ƙuri’a a matsayin ”tsutsar” da ke yi wa harkokin siyasar ƙasar tarnaƙi.
Read Also:
Kwamishinan hukumar mai lura da jihar Rivers Johnson Alalibo Sinikiem, ne ya bayyana haka ranar Litinin a birnin Fatakwal a lokacin da ya halarci taron da ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasar ta shirya.
Mista Sinikiem ya ce hukumar ta sha wayar da kan matasan ƙasar musamman a yankunan karkara da su lura tare da kai rahoton duk wanda suka samu da laifin saye da sayar da ƙuri’a a lokacin zaɓukan ƙasar da ke tafe.
A ranar 25 ga watan Fabrairu ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya