Maganar Inganta Sinadarin Uranium Batu ne na Gaske – Iran

 

Iran ta haƙiƙance cewa ‘yancinta na ci gaba da inganta sinadarin Uranium domin shirinta na nukiliya ba abu ne da za a yi wata yarjejeniya a kansa ba.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aaraqchi, ya ce: “Abin da yake tabbas shi ne cewa batun inganta sinadarin uranium na Iran haka yake, sannan abu ne da aka lamunta kuma batu ne na gaske, kuma a shirye muke mu kwantar hankalin masu damuwa a kai hankali.

“Amma maganar inganta sinadarin ba abu ne da za a yi wata yarjejeniya a kansa ba samsam.”

Kalaman na Iran sun zo ne kafin fara zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka a ranar Asabar mai zuwa.

Shugaba Trump ya yi barazanar tarwatsa tashoshin nukiliyar Iran da bamabamai idan har ta kafe cewa sai ta haɗa makamin na ƙare-dangi.

Iran ta ce shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, amma hukumar nukiliya ta duniya IAEA ta ce Iran din ta inganta sinadrin Uranium da take da shi zuwa kusan matsayin wanda za a iya haɗa makami da shi.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here