Gasar da ‘Yan Najeriya su ke yi a Kasashen Waje, Alama ce ta Ingantaccen Ilimin da su ke Samu a Najeriya – Shugaba Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanayin gasar da ‘yan Najeriya su ke yi a kasashen waje, alama ce ta ingantaccen ilimin da su ke samu a Najeriya kafin su fita daga kasar.

Ya bukaci ‘yan Najeriyan da su ke riskar kawunansu a kasashen waje su yi kokarin ganin sun kiyaye dokokin kasheshen.

Shugaban kasan ya yi wannan furucin ne yayin taro da karamin ministan harkokin kasashen waje na daular larabawa, UAE Shaikh Shakboot Alnahyan a ranar Juma’a.

Faransa – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gasar da ‘yan Najeriya suke yi a kasashen waje alama ce ta ingantaccen ilimin da suke samu kafin su bar kasar, jaridar The Punch ta rawaito.

Sakamakon hakan ya sa ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi kokarin kiyaye dokokin kasashen da su ke zama.

Shugaban kasan ya fadi hakan ne yayin taro da karamin ministan harkokin kasashen waje na daular larabawa, Shaikh Shakboot Alnahyan, a Paris ranar Juma’a.

Mai ba shugaban kasan shawarwari na musamman akan harkokin yada labarai, Femin Adesina ne ya bayyana hakan a wata takarda mai taken ‘Gasar ‘yan Najeriya a ciki da wajen kasar, Shugaba Buhari ga ministan UAE.’

Buhari ya ce ‘yan Najeriya sun karade duniya

Adesina ya yanko inda Buhari ya ke cewa:

“Yan Najeriya su na nan ko ina, kuma su na ta gasa. Kuma gasar a gida take farawa inda su ke samun ingantaccen ilimi sai su koma kasuwanci daga nan kuma su zarce kasashen waje.”

“Shugaban kasa ya shawarci ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da su kiyaye kansu daga karya dokokin kasashen da suke aiki ko kuma sana’o’i.”

Ya amince da bukatar UAE ta hada kai da Najeriya a bangarorin harkokin tattalin arziki, noma, masana’antu da samar da riga-kafin annobar COVID-19.

A bangaren minista Alnahyan, ya ce kasar sa tana matukar yabon mulkin shugaba Muhammadu Buhari, saboda jajircewarsa wurin ciyar da kasar gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here