Ingila za ta Samu Gurbi Idan ta Doke Italiya a Gasar Cin Kofin Turai
Tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta samu gurbin shiga gasar cin kofin Turai, da zarar ta doke Italiya ranar Talata a Wembley.
Ingila da Italiya za su fafata a wasa na shida-shida a rukuni na uku, domin neman gurbin shiga Euro 2024, wadda Jamus za ta karbi bakunci.
Ingila ce ta daya a rukunin da maki 13, bayan wasa biyar, sai Italiya ta biyu mai maki 10.
Cikin watan Maris Ingila ta je Italiya inda ta yi nasara da ci 2-1 a karawar rukuni na uku, karon farko da Ingila ta yi nasara a Italiya a cikin shekara 62.
A makon jiya Italiya ta doke Malta, wadda take ta karshe a rukunin, hakan ya kara bai wa Italiya kwarin gwiwa kan fuskantar Ingila.
A Euro 2022 ne, Italiya ta yi nasara kan Ingila a bugun fenariti a Wembley inda ta lashe kofin.
Bayani kan tawagar Ingila da ta Italiya
Babu wasu ‘yan wasan Ingila da suka sake jin rauni kafin wasan da za ta karbi bakuncin Italiya.
Wadanda tun farko ke jinya, sun hada da Bukayo Saka da Luke Shaw da kuma Ben Chilwell.
Read Also:
Ana sa ran Gareth Southagate zai yi amfani da ‘yan wasan tsakiya da suka hada da Jordan Henderson da Declan Rice da Bellingham ko kuma Trent Alexander-Arnold, wanda ya tsare baya a wasan sada zumunta da Austarlia ranar Juma’a.
Rashin Saka zai samar da gurbin ‘yan wasa biyu da za su kasance masu cin kwallo, idan Ingila ta sauya salo, wato ta sa Marcus Rashford da James Maddison.
Shi kuwa Phil Foden zai buga daga gaba amma zai rika jan kwallon daga gefen fili.
Tawagar Italiya ta umarci Sandro Tonali da Nicolo Fagioli da dan wasan Aston Villa, Nicolo Zaniolo, su koma gida cikin makon jiya, bayan an zarge su da laifin karya dokar caca.
Kocin Italiya, Luciano Spaletti na amfani da salon wasan 4-3-3 tun bayan maye gurbin Roberto Mancini, wanda ke amfani da Domenico Berardi a matsayin mai cin kwallo, da ke jan tamaula daga gefen hannun hagu.
Karawa tsakanin Ingila da Italiya
Bayan da Ingila ta je ta ci Italiya a Naples cikin watan Maris, yanzu tana fatan yin nasara gida da waje a karon farko tun bayan 1940.
A wasa 32 da suka fuskanci juna a baya, Ingila ta yi nasara a wasa tara da canjaras tara, Italiya ta ci fafatawa 13.Karawa tsakanin Ingila da Italiya
Bayan da Ingila ta je ta ci Italiya a Naples cikin watan Maris, yanzu tana fatan yin nasara gida da waje a karon farko tun bayan 1940.
A wasa 32 da suka fuskanci juna a baya, Ingila ta yi nasara a wasa tara da canjaras tara, Italiya ta ci fafatawa 13.