An Samu Damuwa Yayin da Injin Jirgin Sama ya Kama da Wuta a Legas
An samu tashin hankali yayin da wani jirgin sama ya samu tasgaro a sama a wani yankin jihar Legas.
An ruwaito cewa, jirgin ya samu matsala, inda wani injinsa ya kama da wuta yayin da yake shirin sauka a Legas.
Hakazalika, an ce fasinjoji sun sauka lafiya, kuma ba su shiga wani tashin hankali ba, kana an ba su hakuri.
Legas – An dakile wani babban hatsarin jirgin sama a lokacin da wani jirgin sama na Overland Airways ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas daga filin jirgin sama na Ilorin a jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba inda daya daga cikin injunan jirgin ya kama wuta a sama a lokacin da jirgin ke tunkarar filin jirgin, Daily Trust ta ruwaito.
Fasinjoji 33 dake cikin jirgin sun sauka lafiya a sashen filin jirgin sama na kasa da kasa.
Read Also:
An samu labarin cewa Matukin Jirgin na ATR-42 ya ayyana ‘May Day’ wanda a lafazin sufurin jiragen sama ke nuni da halin neman taimakon gaggawa yayin da hukumomi a filin jirgin suka tanadi dukkan matakan gaggawa yayin da ma’aikatan ke kokarin sarrafa jirgin.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce fasinjojin sun natsu a lokacin da ake gudanar da aikin ceton.
Kamfanin ya ce:
“Overland Airways na son sanar da jama’a cewa jirginsa OF1188 daga Ilorin zuwa Legas ya gamu da wani yanayi mai zafi da ba a saba gani ba a daya daga cikin injunansa a yau Laraba 15 ga watan Yuni, 2022 da misalin karfe 7:50 na dare.
“Wannan ya faru ne a lokacin da jirgin ke gab da sauka kuma jirgin ya sauka lafiya yayin da ma’aikatan jirgin suka aiwatar da dabarar tsarinsu kan irin wannan yanayi mara kyau.”
Hakazalika, kamfanin ya kuma ba fasinjoji hakuri bisa rashin jin dadin da aka samu, sannan ya ce zai kula da dakile faruwar hakan a nan gaba.