Jam’iyyar APC Zata Sanar da Abokin Tafiyarta Yau ko Gobe

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC zai sanar da abokin tafiyarsa yau ko gobe.

Alamu sun nuna cewa Bola Tinubu ya yanke shawarar zaben Musulmi daga Arewacin Najeriya.

Daga cikinsu akwai Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon gwamnan Borno.

Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai sanar da abokin tafiyarsa ranar Alhamis, 16 ga Yuni, rahoton Vanguard.

Jaridar ta kara da cewa da alamun Tinubu ya yanke shawaran zaben Musulmi.

Amma Legit Hausa ta tattaro daga tsohon Shugaban matasan jam’iyyar APC kuma hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Isma’il Ahmad, ya bayyana cewa an zabi wanda zai zama mataimakin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Barista Isam’il Ahmad wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook yace mutane su daina yada jita-jita, aikin gama ya gama, sanarwa kawai ya rage.

Yace:

“Game da abokin tafiyar Jagaban, an yanke shawara tuni. Saboda haka ku daina yada jita-jita da bayyana ra’ayoyi. Za’a bayyana komai ranar Juma’a Inshaa Allah.”

Wadanda ake sa rai sune:

– Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan jihar Kano

– Kashim Shettima, Tsohon Gwamnan jihar Borno

– Alhaji Kabir Ibrahim Masari, wani dan yankin Shugaba Buhari

– Dr. Ibrahim Bello Dauda, tsohon sakataren Buhari Support Group (BSG) kuma abokin Shugaba Buhari tun yana jam’iyyun ANPP da CPC.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here