Ya Kamata IPOB ta Jagoranci Almajiranta a Zanga-Zangar Lumana Zuwa Abuja – Ohanaeze Ndigbo Worldwide

 

An nemi ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) da su daina tursasa dokar zaman gida a kudu maso gabas.

A cewar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ya kamata IPOB ta jagoranci almajiranta a zanga-zangar lumana zuwa Abuja.

Kungiyar ta ce idan membobin IPOB miliyan 60 kamar yadda shugabannin suka fadi za su iya mamaye Abuja, hakan zai tilasta masu bayyana Nnamdi Kanu.

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta aika da sako zuwa ga haramtaciyyar kungiyar nan ta ‘yan asalin Biafra (IPOB).

Kungiyar ta kabilar Igbo ta nemi kungiyar da aka haramta ta daina tursasa dokar zaman gida a kudu maso gabas, The Cable ta rawaito.

Ku tuna cewa kungiyar ta yi barazanar kulle yankin idan gwamnatin tarayya ta gaza gabatar da Nnamdi Kanu, jagoranta, a gaban kotu a ranar 21 ga watan Oktoba.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, Okechukwu Isiguzoro, babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ya ce za a tilastawa gwamnatin tarayya bayyana Nnamdi Kanu idan ‘yan kungiyar IPOB miliyan 60 za su iya mamaye Abuja.

Ku tuna cewa Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Ohanaeze a baya tayi kira ga mutane da su yi watsi da dokar zama a gida.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here