Dokar ‘Yan IPOB na Hana Fita: An Bankawa Motar Kayan Miya Wuta a Jahar Enugu
Har yanzu kungiyar IPOB na hana mutan gari sararawa kowace ranarr Litinin.
Yan kungiyar sun kafa dokar hana fita kowace Litinin har sai an sako shugabansu Nnamdi Kanu.
A yau an kona dukiyar dubban nairori a jahar Enugu.
Enugu – Wasu batagari sun bankawa motar dake dauke da kayan miya wuta a jahar Enugu ranar Litinin bayan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ta kafa dokar hana fita.
Read Also:
Bisa hotunan da suka yadu a kafafen sadarwa, motar na dauke da tumatur, kubewa, da sauran kayan abinci. Daily Trust ta rawaito cewa an bankawa wannan mota wuta ne a tashar Edem, Ibeagwa, karamar hukumar Enugu ta yamma.
Jama’an gari suka kira jami’an kwana-kwana wadanda suka kashe wutar.
Wani mai idon shaida ya bayyana cewa:
“Wannan babbar asara ce da bai kamata ace ta faru ba da mutanenmu sun yi tunani .”
Hukumar yan sandan jahar tace bata kama kowa ba har yanzu cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika, amma dai an kaddamar da bincike.